<?xml version="1.0" encoding="UTF-8"?><song><hymn_number>285</hymn_number>
<lyrics>[V1]
 1) Ku yi ƙarfin zuciya cikin Allahnmu.
 Shaiɗan da mala'ikunsa sun kewaye mu duk.

[V2]
 KORUS
 Sai mu tsaya cikin ikon Yesunmu
 Sai mu riƙa ƙaunar Almasihu Mai Ceto.

[V3]
 2) Ga shi, Shaiɗan yana nan cikin duniya,
 Yana fushi in ya ga mu bayin Yesu ne.
 Korus

[V4]
 3) Kome yawan wahala da Shaiɗan ya kawo,
 Sai mu bi Ubangiji, zai ba mu nasara.
 Korus

[V5]
 4) Idan muna jurewa zuwa matuƙa,
 Almasihu za ya ba mu kambin nasara.
 Korus</lyrics>
<title>Ku Yi Ƙarfin Zuciya Cikin Allahnmu LW285</title>
</song>